Kannywood

Bikin karrama ‘yan Kannywood


Ana sa ran manya manyan baki daga cikin da kuma wajen Najeriya za su halarci bikin da za a yi yau Asabar

A Najeriya, ranar Asabar ne ake bikin bayar da kyautuka ga ‘yan fim din Hausa, wato Kannywood wadanda suka yi fice a shekarar 2015.

Bikin wanda ake yi a karo na uku a Abuja zai kuma duba rawar da ‘yan Fim suka taka a shekara 25 da aka yi da samar da Kannywood. Shugaban kwamitin da ya hada bikin, Dr Ahmad Muhammad Sarari, ya ce za a bayar da kyautuka ga gwarzon dan Fim na shekarar 2015 da gwarzuwa da gwarzon Darakta da Fim din da ya fi yin ma’ana da sauransu.
A shekarar da ta gabata dai, fitaccen jarumi Sadiq Sani Sadiq ne ya lashe kyautar jarumin jarumai, yayin da Hadiza Aliyu Gabon ta lashe kyautar jarumar jarumai.
Fina-finan na Hausa na ci gaba da taka rawa wajen nishadantar da mutane da kuma samar da kudaden shiga ga masu yin su da kuma gwamnati. Sai dai masu yin Fina-finan na shan suka saboda tarbiyyar da ake zargin su da batawa.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.