
Saddiq Sani Saddiq da Nafisa Abdullahi ne suka lashe kyautar jaruman shekarar 2015.
An dai bayar da kyautukan ne ga jarumin jarumai da takwararsa, jarumar jarumai da gwarzon darakta da sauransu.
A cikin wadanda aka bai wa karrama har da marigayi Tijjani Ibrahim, daya daga cikin manyan daraktocin da suka fi yin suna a masana’antar ta Kannywood.
Sai dai iyalansa ba su halarci taron ba, lamarin da ya sa jarumi Ali Nuhu ya karbi kyautar a madadinsa.
Iyalan Tijjani Ibrahim din dai sun ce ba a kyauta musu ba
Ali Nuhu ne ya karbi kyauta a madadin Tijjani Ibrahim.
Babban dan marigayin Salim Tijjani Ibrahim ne ya rubuta wata wasika ga wadanda suka shirya bikin ta shafinsa na sada zumunta da muhawara na Facebook, inda ya ce ba a kyauta musu ba domin kuwa ba a gayyace su wajen bikin ba.
Amma a hirar da ya yi da BBC, Dr. Ahmed Sarari, babban jami’in gudanar da taro ya ce sun aika wa da iyalan takardar gayyata, ba su san cewa ba ta kai gare su ba.
Tijjani Ibrahim na daya daga cikin fitattun masu ba da umarni a Kannywood wanda ya rasu a shekara ta 2002.
Add Comment