Uncategorized

BH: Sojoji sun ceto mutane 900 a Kamaru

Ministan tsaron Jamhuriyar Kamaru ya ce dakarun sojin kasar sun kashe ‘yan kungiyar Boko Haram 100 a wani samame da suka kai musu.
Joseph Beti Assomo, wanda ya bayar da sanarwar a gidan talabijin na kasar, ya ce dakarun sun kuma ceto mutane 900 da ‘yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta ce, “”An gudanar da samame na musamman domin kakkabe ‘yan Boko Haram tsakanin ranakun 26 zuwa 28 ga watan Nuwamba a kan iyakarmu da Najeriya, kuma an kashe ‘yan Boko Haram 100”.
Ya ce sun kwato makamai da alburusai da dama, sannan suka samu tutocin kungiyar IS a wurin da suka kai samamen, ko da ya ke bai yi karin bayani ba.
An kai hari a arewa mai nisa
Hakan na faru ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga biyu sun kai hari a arewacin kasar a daren ranar Talata, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla uku.
Kazalika an kai makamancin wannan harin a garin Waza da ke da yankin arewa mai nisa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane shida — ciki har da maharan guda uku.
Jami’an tsaro sun kashe ‘yar kunar bakin wake ta uku a yayin da take kokarin tayar da bam din da ke jikinta.