‘Beraye Da Kwari Sun Hana Shugaba Buhari Shiga Ofishinsa Dake Villa

29

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Haji Shehu

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun bayyana cewar, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai shiga babban ofishinsa ba sakamakon barnar da beraye da kwari sukayi a ofishin, yayinda yake jinya a kasar Birtaniya.

 

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 906

Majiyar mu ta ruwaito cewar kakakin shugaban kasa Malam Garba Shehu, ya tabbatar da cewar shugaba Buhari zai ci gaba da aiki a gida har zuwa lokacin da za’a kammala yan gyare-gyaren ofishin nasa.

Fadar ta shugaban kasa tana da ofisoshi biyu, daya a hade da gida, daya kuma daga wajen gidan shugaban kasa.

Babban ofishin dake wajenne Berayen suka lalata, wanda hakan ya tilasta shugaban komawa karamin ofishin dake hade da gida.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.