-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

BBC Ta Ja Kunnen Masu Bata Mata Suna


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A yakin da BBC take yi da yada labaran boge, kafar ta gano wani shafi da aka bude da sunan ”Bbc hausa nigeria” a shafin Facebook inda shafin ke karkatar da hankulan jama’a zuwa ga labarun karya da sunan kafar BBC Hausa.

Akwai irin wadannan shafukan a kafafen sada zumunta na Intanet da dama, masu yada labaran karya da sunan BBC Hausa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 659

- Advertisement -

Wani labari da irin wadannan shafuka na boge suka buga shi ne labarin da aka alakanta sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso yana zagin wasu ‘yan siyasa da masu sarauta na jihar Kano.

BBC Hausa ta nisanta kanta daga irin wadannan labaran da kuma makamantansu a irin wadannan shafukan na boge.

BBC za ta dauki matakan da suka dace wurin dakile irin wadannan aikace-aikace da kuma hukunta masu aikata su.

Shafin BBC Hausa na ainahi ya fita daban kuma za a ga alamar maki shudi a gefen shafin daga hannun hagu kamar haka:

BBC

Wata alama da za a kara tabbatar da shafin BBC Hausa na ainahi za a ga cewa akwai sama da mutum miliyan biyu da suke bin wannan shafi.

Shima shafin BBC Hausa na Twitter za a ga alamar maki shudi a gefen shafin daga hannun hagu kamar haka;

BBC

Hakazalika shafin Twitter na BBC Hausa za a ga sama da mutane dubu 300 ne ke bin wannan shafin.

Yada labaran boge ba sabon abu ba ne musamman a shafukan sada zumunta.

Akan yi amfani da shafuka irin su Facebook da Twitter domin yada irin wadannan labaran.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: