News

Bazan Damu Ba Idan An Saka Ni A Jahannama, Tunda Yawancin Mutane Za Su Kasance Ne A Cikin Ta – Elon Musk

Mai kudin duniya, Elon Musk, ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter wanda ya girgiza mabiyansa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu.

Musk ya rubuta cewa ya kusa mutuwa Koda dai bai bayar da cikakken bayani kan halin da yasa shi fadin haka ba, mai kudin ya nuna rayuwarsa na gab da zuwa karshe.

Wani mabiyinsa mai suna Almisehal wanda ya nuna damuwa game da rayuwar biloniyan ya ce ba zai mutu ba kafin lokacinsa.

Cikin haka sai ya kuma ya tambayi Musk kan ko har yanzu bai gane cewa akwai mahallicin duniyan nan ba, sannan ya bukaci da ya bayyana hakan idan har ya gano hakan kafin fitar ransa.

Da yake mayar masa da martani, Elon Musk ya fada masa cewa shi bai damu ba don an saka shi a wutar jahannama.

Ga yadda hirar tasu ta kaya:

@Almisehal: “Ba za ka mutu ba kafin ranar ka Elon. “Duk da haka, kai ka kasance mutum ne na musamman a wannan duniyar.

Abu daya nake mamaki: A matsayinka na haziki, ba ka gano cewa akwai babban mahaliccin wannan duniyar ba tukuna?

“Idan ka yi, ka tabbata ka furta wannan kafin bugun zuciyarka ta karshe. “Allah ya albarkace ka.”

elonmusk: “Na gode da sa albarkar, amma ban damu da shiga jahannama ba, idan har wannan ne makoma ta, tun da yawancin mutanen da aka haifa za su kasance a wurin.”

Meye Ra’ayin ku?

Tags