Bayyana Tsaraici Ba Shi Ne Wayewar Mace Ba, Wayewa Shi Ne Ki Zamo Mai Bin Dokokin Allah


0 739

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Salma Edrees Maimurjani

Wannan shine kamalar mace a addinin musulunci kuma haka ya kamata kowacce mace ta kasance cikin hijabi musamman matan shugabanni da suke shiga cikin maza ko na ce suke siyasa babu kamun kai. Wasu ma babu mayafi har ka ga suna hada hannu da maza suna gaisawa sabida wai su a waye suke kuma haka ba wayewa bane hajilci ne tsantsa!!!

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 17

-Advertisement-

Kuma duk suturar da take rufe jiki gaba daya ba tare da ta nuna surar jikin mace ba kuma ya kasance mai duhu mai kauri, to shi ma hijabi ne amma matan shugabanni a yanzu ba sa saka sutura mai yalwa ballantana su saka hijabi irin na addinin musulunci.

Allah ka yi wa wannan matar gwamnan (Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya) albarka ka sa ta gama da duniya lafiya, ta kasance mai riko da addininta mai kishin kanta da na mijinta.

Allah ka sa sauran mata mu runka koyi da halayen mata nagari. Amin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.