Fitaccen mawaƙin Nijeriya ɗin nan, David Adeleke, ya sanar da tallafin naira na gugar naira har miliyan 250 ga gidajen marayu na ƙasar nan.
Kwanaki biyu da su ka gabata ne a ka tarawa Davido kimanin naira miliyan 2000 bayan da ya nemi a tara masa ya ɗauki motarsa.
Ai kuwa a yau Asabar sai ga Davido ɗin ya sanar a wata sanarwar da ya fitar cewa ya bada tallafin miliyan 250 domin taimakawa marayu a ƙasar nan.
Da ma mawaƙin ya baiyana cewa zai bada tallafin kuɗaɗen da a ka haɗa masa ga marasa ƙarfi.
Ya kuma baiyana cewa ya kafa kwamiti don tantance gidajen marayun da za su ci gajiyar kudin a fadin kasar nan.
Add Comment