Kannywood

Baya Ga Sana'ar Man Fetur, Ba Sana'ar Da Takai Fim Samun Kudi – Inji Zango

Baya Ga Sana’ar Man Fetur, Ba Sana’ar Da Ta Kai Fim Samun Kudi, Cewar Adam A. Zango
Daga Aminu Dankaduna Amanawa
Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam A Zango ya bayyana cewa, baya ga sana’ar man fetur, ba sana’ar da ta kai sana’ar fim samun kudi.
 
Adam A Zango ya bayyana haka ne, a zantawarsa da Gidan Rediyon BBC.
Jarumin ya kara da cewa fim din Gwaska na daga cikin fina-finan da ya samu kudade a dukkanin fina-finnan da ya aiwatar, Kana ya bayyana wakar “Gumbar Dutse” a matsayin wakar dake zama bakadamiyar sa daga cikin wakokinsa.