Labarai

Batun yiwa ‘yan jarida hasafi

Daga Jaafar Jaafar
Kusan shekara hudu da ta gabata na yi wasu rubututtuka da su ka tada tarnaki, har ta kai ga wani gwamna ya kirani a waya yana neman na tsagaita wuta.

“Muna neman mu yi sulhu ne tsakanin… (wane da ne), kuma mun yi ‘meeting’ mun tattauna cewa idan ba ka tsagaita wuta ba, sulhun ba zai yiwu ba. Don Allah ina neman alfarma ka tsaya haka,” gwamnan ya fada min ta waya.

Bayan ya roki wannan alfarma, sai ya ce: “kanina zan aiko wane da sako…”

Caraf sai na katse shi, na ce masa: “Ranka ya dade ba sai ka ba ni komai ba…”

Shi ma kuwa sai ya katse ni, ya ce “Ni ba yayanka ba ne? Zan aiko wane da sako,” sai ya katse wayar.

Abin da na yi, sai na kira wanda ya ce zai aiko da sakon, na ce masa: “Alhaji wane, don Allah ka samu Gwamna, ka yi masa bayani cewa na sha alwashin a ko ina zan iya alwala na dafa Alqur’ani cewa babu wanda ya taba ba ni kudi don na yi wannan rubutun ko kuma don na ki yin wannan rubutun. Don Allah ka ce masa na gode.”

Har ga Allah daman ban yi niyyar na sake ci gaba da wannan rubutu ba. Kuma ban sake yi ba.

Haka kuwa aka yi, dan sako ya fadawa gwamna. Abin ya cika gwamna da mamaki. Duk inda ya je cikin abokansa gwamnoni sai ya yabe ni. Akwai lokacin da ya tara manya-manyan yan jarida na kasar nan don duba ayyuka a jiharsa, ya yi amfani da damar ya yi ta yabo na, duk da ba na wajen.

Ba wai yabon kai ba, gwamnoni da yawa da ministoci da manyan jami’an gwamnati da na sani idan na kira su a waya zai wuya ba su dauki wayata ba, ko kuma su kirani in sun samu sukuni. Ko zuwa na kasar Ingila, akwai gwamnoni da ministoci da su ka kira ni a waya don jajanta min abinda ya faru, kuma su ka nemi na kira su in ina da wata bukata. Wallahi har yau babu wanda na kira don neman bukata, sai dai don neman labari.

Idan ka kare mutuncinka a aikin jarida, kana zaune za ka ga alherin aikin yana zuwa maka. Idan ka yi kokari ka iya aiki kuma ka san mutane (contacts) to ka gama koyon aikin jarida. Idan ka san mutane, kai tsaye za ka tuntube su don jin ainahin abinda ya faru. A sanadiyar waccan alaka da na kulla da wannan gwamna, na samu alheri da dama wajen saka talla a shafin kamfaninmu.

Ba wai ina nufi ni waliyyi ne ba, a’a. Ina dai kokarin tsarkake aikina daidai gwargwado. Wasu za su yi mamakin to ta yaya Jaafar ya ke rayuwa? Babban sirrin shi ne, sana’a. Jaridar Daily Nigerian tana samun talla iri-iri ta miliyoyin nerori daga kamfanoni masu zaman kan su da ma’aikatun gwamnati da kuma gwamnatocin jihohi. Akwai kuma talla da kamfanin Google Adsense ya ke saka mana, ita ma tana kawo mana daloli daidai gwargwado.

Baya da wannan, ina cajin kudi don na rubutawa mutum jawabi (speech) ko ra’ayi (opinion) ko na gyara wanda aka rubuta — abin da mu ke kira “PR consultancy”.

Mu dawo batun yiwa ‘yan jarida hasafi (honorarium). A hakikanin gaskiya yanayin Nigeria ne ya sanya kusan a kowacce sana’a mutum yake yi, in an yi masa hasafi zai karba. Kamar yadda akasarin gidajen rediyo da jaridu ba sa samun cinikin da zai rike su yadda ya kamata, haka su ma ba sa iya biyan ma’aikatansu albashi maitsoka da zai dauke musu bukatunsu. Kuma matsalar ta shafi ko ina ne, ba wai aikin jarida shi kadai ba. Abinda za’a fahimta a nan shi ne, bawa danjarida hasafin kudin mota ba shi ne yake hana shi fadar gaskiyar al’marin abinda ya faru ba.

A kasashen da su ka ci gaba kuma, sun fi damuwa da abinda ake cewa “chequebook journalism” wanda mutane ke neman danjarida ya biya su kafin su ba shi labari ko ya yi masu interview. Allah daya gari bambam! Amma fa ko a kasashen Turawa, akwai yadda ake yi ana biyan editoci ta hanyar wasu ‘yan harkalla (lobbyists) don buga labari ko sanya shi a rediyo ko talabijin.

A karshe ni ban ga laifi ba don shirin fim ya fitar da abin da a zahirance yana faruwa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: