Labarai

Barista Aisha Wakili, Mama Ga ‘Yan Boko Haram

A wata tattaunawa da kafafen yada labarai da tayi a baya, Aisha Wakili ta tabbatar da cewar Shugaban Boko Haram na farko Muhammad Yusuf da Mataimakin Shi Abubakar Shekau, babu inda suke hira a garin Maiduguri sai a gidan ta, su kan ci abinci su yini suna hira a gidanta.

Aisha Wakili wacce asalin ta Inyamura ce daga kudancin Nijeriya, ta karbi addinin Musulunci ne lokacin da take karatun aikin Lauya a Jami’ar Maiduguri, inda ta zabi sunan Aisha a matsayin sabon sunan ta na Musulunci, kuma ta auri Barista Muhammad Wakili Ghana, ma’aikaci a Kotun daukaka kara da ke Maiduguri.

 

Aisha Wakili ta bayyana ‘ya’yan Boko Haram a matsayin mutane masu saukin kai da ladabi, domin ita kanta suna kiran ta da suna Mama, sai dai kuma suna da tsanani a wajen kishin Addinin Musulunci, sannan suna adawa da sunan da aka kakaba musu na Boko Haram, domin halastaccen sunan su shine Jama’atu Ahalus Sunnah Lil Da’awati Wal Jihad.

A shekarar 2016 Rundunar Sojojin Nijeriya Karkashin Jagorancin Janar Tukur Yusuf Buratai ta gayyaci Aisha Wakili domin amsa wasu tambayoyi dangane da harkokin Boko Haram.