Barcelona na sa ran Neymar zai koma atisaye a ranar Laraba, amma a shirye take ta yi karar Paris St-Germain idan har ta biya Yuro miliyan 222 kudin ka’ida da ta saka ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan Brazil din.
Ana alakanta Neymar dan wasan Brazil mai shekara 25, da cewar zai koma buga gasar kwallon Faransa, kuma a ranar Talata ya kamata ya koma Spaniya daga China.
Rahotanni na cewa dan kwallon zai je Qatar a makonnan domin PSG ta duba lafiyarsa. A makon jiya shugaban kungiyar Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya ce Neymar zai ci gaba da taka-leda a Camp Nou a bana.
Add Comment