Labarai

Barcelona: ‘Yansanda sun harbe mutum biyar da ake zargi

Yansanda a kasar Spaniya sun yi wani gagarumin farmaki kan ‘yan ta’adda, bayan wasu harbe-harbe a wurin shakatawa na garin Cambrils dake kudancin birnin Barcelona.

Mahukunta sun ce , an harbe har lahira mutane biyar da ake zargi da ayyukan ta’addanci, daure da wata damarar kunar bakin wake.

An danganta faruwar lamarin da mumman harin baya-bayan nan da aka kai a birnin Barcelona, lokacin da maharan tuka babbar wata motar ldaukar kaya ta cikin taron jama’a a sanannen titin Las Ramblas na birnin.

 

Mutum 13 ne suka mutu yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata babbar mota ta afka wa masu yawon bude ido a wurin shakatawa na Ramblas da ke garin Barcelona.

‘Yan sanda kasar Spaniya sun ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka gargadi mutane su nisanci dandalin shakatawar a kusa da Placa Catalunya.

Rahotanin da ganau suka yada sun tabbatar da mutane na gudun ceton rai, inda suke neman mafaka a kantinan da ke kusa da wurin da wuraren shan Gahawa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hukumomin agaji sun bukaci a rufe tashar mota da ke kusa da wurin da ta jirgin kasa.

Fira ministan kasar Spaniya , Mariano Rajoy, ya ce ‘yan ta’addar masu jihadin ne ke da alhakin kai hari a birnin na Barcelona, inda mutane fiye da dari suka samu raunuka.

Ya ce ” Ina son kalamai na na farko a daren nan a Barcelona su kasance na nuna jimami da nuna goyon baya ga wadanda harin ya shafa, ina kuma son in yi nuni da goyon bayan daukacin yan kasar Spaniya”

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.