Yansanda a kasar Spaniya sun yi wani gagarumin farmaki kan ‘yan ta’adda, bayan wasu harbe-harbe a wurin shakatawa na garin Cambrils dake kudancin birnin Barcelona.
Mahukunta sun ce , an harbe har lahira mutane biyar da ake zargi da ayyukan ta’addanci, daure da wata damarar kunar bakin wake.
An danganta faruwar lamarin da mumman harin baya-bayan nan da aka kai a birnin Barcelona, lokacin da maharan tuka babbar wata motar ldaukar kaya ta cikin taron jama’a a sanannen titin Las Ramblas na birnin.
Mutum 13 ne suka mutu yayin da wasu 32 suka jikkata bayan wata babbar mota ta afka wa masu yawon bude ido a wurin shakatawa na Ramblas da ke garin Barcelona.
‘Yan sanda kasar Spaniya sun ce mutane da dama sun jikkata, yayin da aka gargadi mutane su nisanci dandalin shakatawar a kusa da Placa Catalunya.
Rahotanin da ganau suka yada sun tabbatar da mutane na gudun ceton rai, inda suke neman mafaka a kantinan da ke kusa da wurin da wuraren shan Gahawa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito hukumomin agaji sun bukaci a rufe tashar mota da ke kusa da wurin da ta jirgin kasa.
Fira ministan kasar Spaniya , Mariano Rajoy, ya ce ‘yan ta’addar masu jihadin ne ke da alhakin kai hari a birnin na Barcelona, inda mutane fiye da dari suka samu raunuka.
Ya ce ” Ina son kalamai na na farko a daren nan a Barcelona su kasance na nuna jimami da nuna goyon baya ga wadanda harin ya shafa, ina kuma son in yi nuni da goyon bayan daukacin yan kasar Spaniya”
Add Comment