Barcelona ta ci International Champions Cup, bayan da ta doke Real Madrid da ci 3-2 a karawar da suka yi a Amurka.
Wannan ne karo na biyu da kungiyoyin Spaniya masu buga wasan hamayya da ake kira El-Clasico suka kara ba a cikin kasar ba, tun bayan wanda suka yi a 1991.
An buga karawar a filin wasa na Hard Rock da ke Miamin Amurka wanda ‘yan kallo 66,014 suka kalli kwallayen da Lionel Messi da Ivan Rakitic suka fara ci wa Barcelona.
Daga baya ne Real Madrid ta farke ta hannun Mateo Kovacic da kuma Marco Asensio.
Barcelona ta ci kwallo na uku ta hannun Gerard Pique a bugun tazara da Neymar wanda PSG ke son dauka ruwa a jallo ya buga.
Barcelona ta yi nasarar cin kofin ne bayan da ta doke Juventus da Manchester United da Real Madrid a gasar.
Ita kuwa Madrid din ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da Manchester City da kuma Barcelona.
Add Comment