Barcelona da Real Madrid za su kece raini a wasan hamayya da ake kira El-Clasico a gasar International Champions Cup a ranar 30 ga watan Yuli.
Kungiyoyin da ke buga gasar Spaniya za su fafata ne a filin wasa na Hard Rock da ke Miami a birnin Floridan Amurka.
Wannan ne karo na biyu da Barca da Real za su buga El-Clasico ba a Spaniya ba, na farko shi ne wanda suka kara a Barquisimeto da ke Venezuela a ranar 30 ga watan Mayun 1982.
Kungiyoyin biyu za su sake karawa a ranar 13 ga watan Agusta a Spanish Super Cup wasan farko a Camp Nou, sannan Madrid ta karbi bakuncin wasa na biyu ranar 16 ga watan na Agusta.
Real za ta yi karawa ta uku a wasan International Champions Cup, bayan da Manchester United ta doke ta a bugun fenariti, sannan Manchester City ta zura mata 4-1.
Ita kuwa Barcelona ta ci Juventus 2-1, sannan ta doke Manchester United 1-0.
Souce in bbchausa
Add Comment