Barcelona ta bai wa Neymar damar barin kulob din a daidai lokacin da ake ganin dan kwallon zai koma Paris St-Germain a kan kudi fan miliyan 198.
Dan wasan na Brazil, mai shekara 25, ya shaida wa abokan wasansa cewa yana son barin kungiyar.
Koci Ernesto Valverde ya bashi damar kada ya yi atisayi domin ya mayar da hankali kan makomarsa.
Akwai yarjejeniya a kwantiraginsa cewa duk kulob din da ke son daukarsa sai ya biya fan miliyan 198.
Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan an ruwaito cewar Barca ta shirya domin ta kai karar PSG domin kaucewa ka’idar kashe kudi wurin sayen ‘yan wasa idan har ta sayi Neymar.
Kuma wannan ya biyo bayan gargadin daukar matakin shari’a da shugaban hukumar gasar La Liga, Javier Tebas, ya yi idan hukumar kwallon kafa ta Turai ta kasa daukar mataki.
Ya kuma ce an sanar da shugaban PSG, Nasser Al-Khelaifi, abubuwan da kungiyar kwallon kafa ta Spaniyar ke da niyyar yi.
Neymar ya koma Barcelona daga kungiyar Santos ta Brazil, a shekarar 2013 kan kudi fam miliyan 48.6, kuma ya sake rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta shekara biyar da kungiyar bayan da ta ci kofinta na zakarun Turai a 2016.
Wasu rahotanni sun ce Neymar zai je Doha, babban birnin Qatar, domin ganawa da shugaban kulob din na PSG.
Souce In Bbchausa
Add Comment