– Sowore yace barayin kasar nan su ka sa Shugaba Buhari rashin lafiya
-Mai Jaridar Sahara Reporters yace kudin da aka sata ya rikitar da Buhari
-Irin satar da aka yi a Gwamnatocin baya dai ya wuce tunanin mutum
Omoyele Sowore yace irin mahaukaciyar satar da aka rika tafkawa a Najeriya ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwanta rashin lafiya.
A wani taro da aka yi a Kent a karshen makon nan Sowore yace Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kwanta ne lokacin da ya fahimci irin satar da aka buga a Najeriya.
Yanzu dai Shugaban kasar ya fara murmurewa.
Yanzu dai har Najeriya ta fita daga jerin kasashen da su ka yi kaurin suna wajen harkar cin hanci da rashawa a Duniya.
Sowore yace dole Kasashen Duniya su taimaka wajen daina boye kudin sata daga Najeriya.
Add Comment