Labarai

Barayin Da Suka Sato Motar Dan Majalisar Tarayya A Abuja Sun Fada Komar ‘Yan Sanda A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin, kwamishinan ‘yan sanda, Alhaji Sanusi Buba ta yi nasarar wasu barayin mota, da shigar manyan kaya, domin yin badda bami, akan hanyar su ta shiga jamhuriyar Nijar, domin cefanar da ita.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isa ne ya yi baje-kolin su a helkwatar rundunar da ke hanyar Daura cikin garin Katsina a yau Litinin.

SP Gambo Isa ya ci gaba da cewa da misalin karfe sha biyu na yau litinin, sakamakon bayanan sirri da suka samu, inda suka samu nasarar cafke wadansu matasa, Aliyu Mohammed, dan shekara, talatin da takwas da haihuwa, dake Sarki Avenue, Kurmin Mashi a jihar Kaduna da kuma Jamilu Tijjani dan shekara talatin da haihuwa, da ke zaune Karshen Waya a Gyadi-gyadi, a cikin Birnin Kano.

Kakakin Rundunar ya kara da cewa rundunar ta samu kiran gaggawa, da misalin karfe bakwai wasu yan fashi, su bakwai dauke da manyan makamai, sun kai hari a gidan wani dan majalisar wakilai, Honarabul Abdullahi Zimbo, Mai wakiltar Dandi Wasagu. Inda suka sato motarsa kirar Toyota Jip, mai lamba ABC 79 GC. An same su da jama, wadda na’ura ce wadda ko ana neman motar da na’ura mai Kwakwalwa ba’a ganin motar.

Wadanda ake zargin sun amsa laifin su, amma sun ce ba su suka sato motar ba, wani ne ya aike su domin fita da ita Jamhuriyar Nijar. Ana ci gaba da bincike domin gano sauran da suka aikata fashin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: