A jiya ne wasu barayi suka shiga gidan daya daga cikin manyan jaruman kannywood wato Bello Muhammed Bello (BMB) inda suka faffasa motarsa suke debi kudi masu yawa.
Jarumin ya bayyana hakanne a shafinsa na sada zumunta da yada manufa wato instagram inda yake cewa:-
- Advertisement -
Na tashi da safe na tarar da an fasa min mota an sacemin abubuwa har da kudade miliyan biyu da kusan dubu dari uku.
Koma waye, Allah na nan kuma Insha Allahu a karo na gaba, Allah ya kiyaye, zaku yi a bakin ranku Insha Allah.
Allah shi ya bani kuma zai kara bani Insha Allah.
Kuma koya sannan wannan jarumin dan a mutum shugaban kasa ne mai ci a yanzu wato General Muhammadu Buhari