Cin Hanci da Rashawa Labarai

Barayi 2 Da Suka Sace Wayoyin Hannu Guda 48 A Katsina Sun Shiga Hannu

Barayi 2 Da Suka Sace Wayoyin Hannu 48 A Katsina Sun Shiga Hannu

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta sanar da kama wasu mashahuran barayin waya biyu wadanda suka shiga wani shago tare da sace wayoyin hannu guda 48.

 

Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.

 

Ya ce an kama wadanda ake zargin, masu shekaru 22 da kuma 23 ne a Katsina a ranar Laraba bisa samun sahihan bayanan sirri.

 

Isa ya ce wadanda ake zargin sun hada baki ne da wani inda suka yi fasa shagon sayar da waya da ke Tsohuwar Tashar Katsina, tare da sace wayoyin hannu guda 48 da aka samu a hannunsu.

 

Ya yi ikirarin cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.

 

Kakakin rundunar ’yan sandan ya ce, za a kamo sauran mutum biyu da suka tsere, sannan a hada su a gurfanar da su a gaban kuliya.