Nasiha

BARAWO YAZAMA SARKI

BARAWO YAZAMA SARKI
Wani barawo ne ya shiga Masallaci dan ya yi sata a tsakiyar dare.
Da shigar sa sai ya ji motsin mutane kusa da Masallacin. Da ya ji sun matso kusa sai ya kabbarta sallah.
Ana haka sai ya ji an bude Masallaci an shigo.
Sai ya yanke shawarar tsawaita Sallah saboda jin tsoro.
Su kuma kawai sai suka share wuri suka zauna suna jiran sa.
A tsorace ya sallama ya waiga don ya ga ko su wane ne.
Ko da ya juya sai ya ga Sarki da tawagarsa.
Kafin ya ce komai sai Sarki ya mika masa hannu suka gaisa, bai san abinda ke faruwa ba. Aka je da shi fada aka kyautata masa har gari ya waye sannan aka yi yekuwa.
Jama’a suka taru sannan sai Sarki ya yi jawabi.
Ya ce, tun da dadewa ina son in aurar da babbar ‘yata.
Kuma na rasa wanda zan aura ma ita domin ina neman na kirki mai jin tsoron Allah.
Amma Liman ya ba ni shawara kuma na yi aiki da ita.
Na samu wannan saurayi a tsakiyar dare shi kadai cikin Masallaci yana sallah a lokacin da duk ire-irensa suna gida suna bacci.
Dan haka na aura masa da ‘yata kuma na yanka masa wani babban gari daga cikin masarautata.
A nan ne fa Barawo ya sunkuyar da kansa yana kuka, yana fadi a zuciyarsa, wannan fa sallar qarya ce na yi Allah ya ba ni wannan alheri.
To, ina ga na yi sallar gaskiya! Ya Allah daga yau na daina duk wani aikin assha, kuma zan riqa sallar dare har iya tsawon rayuwata.

Rubutawa :

Haiman Khan Raees
 @HaimanRaees

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.