Tasi’u Unguwa Uku shaharren mawakine, wanda yayi fice wajen rera wakokin soyayya dana masarauta gamimda siyasa.
A zantawar da Mujalla Fim tayi da wakin tayi ma shi tambayoyi masu yawa ciki harda abunda ya shafi wakarsa ta ‘matar abokina’ da kuma makomarsa awaka zuwa gaba. amma sai ya amsa da cewa:
Wakar Matar Abokina kirkirarra ce wanda duk abinda na fada awakar bai faru ba. kawai wani sabon salone na fadakarwa. domin ana samun haka, matar abokin ka tace tana sonka. kaima ka so ta rashin sani, daka karshe idan taga ka gane ta tayi ma sharri tace kaine kake neman akan kana sane.
Kuma burina akan waka shine, in wa’azantar in nishadantar kuma in fadakar da mutane. amma duk da haka bana so in mutu ina waka. nafiso kafin in mutu Allah ya canja min wata sana’ar amaimakon waka. kuma ba wata matsala da nagani a waka, ra’ayinane kawai haka. bana so in mutu ban daina waka ba. inji mawakiya Tasi’u Unguwa Uku Kano State.
Add Comment