Labarai

Ban yi da-na-sanin furucin da na yi kan rashin lafiyar Buhari ba

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce jikin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi nauyi sosai ta yadda ba zai iya shugabancin kasar nan ba. Don haka, ya kamata ya yi ritaya, ya koma Daura ya zauna.

Gwamnan, wanda ya yi jawabi a Ado-Ekiti a ranar Laraba, ya kuma kekesa kasa ya ce ba zai bada hakuri kan duk bayanan da ya yi dangane da rashin lafiyar shugaban kasa ba.

Fayose ya sha suka tun bayan da Buhari da ya dawo daga jiyya a London. Musamman yadda aka rika kalubalantar sa na ya cika alkawarin kashe kan sa da ya ce zai yi, muddin Buhari ya dawo da ransa.

Sai dai kawai shi Fayose ya karyata cewa ya yi wacan ikirari na alkawarin kashe kan sa da ya ce zai yi.

“Bari na fada maku wata magana. Don me zan kashe kai na? Ni fa ba zan iya kashe kai na saboda uwa ta ba, ballantana wani.” Inji Fayose.

“Kai ni fa ko uwa ta aka tona kabari za a rufe, ba ma zan tsaya kusa da kabarin ba, don kada ma jiwa ta kwashe ni na rifta a ciki.’’

Fayose ya bayar da dalilan abubuwan da su ka faru bayan dawowar Shugaban Kasa a matsayin hujjar sa ta cewa ya yi ritaya haka nan tunda ba zai iya ba.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.