Ban Taba Zaton Ali Nuhu Zai Kai Ni Kotu ba –In Ji Adam Zango


0 520

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fitaccen jarumin fina-finan Hausan nan Adam Zango ya ce ya ji matukar kunya da mutumin da yake kira ubangidansa a masana’antarsu wato Ali Nuhu ya kai shi kara kotu.

Adamu ya ce bai taba tsammanin cewa wani a masana’antar zai iya kai shi kotu balle Ali.

“Ai muna da shugabanni, na yi tsammanin komai ya faru su za a gayawa su sasanta, amma sai aka kai kotu, gaskiya abin ya ban kunya,” in ji Adamu.

A kwanakin baya ne dai jarumi Adam Zango ya wallafa wani sako inda ya yi ikirarin cewa tun da Ali ya sa aka zagi mahaifiyarsa shi ma sai ya rama.

Daga bisani ne Ali ya kai Adamu kotu, inda har aka aike wa Zangon sammaci.

Duk da yake a yanzu an sasanta jaruman biyu, sai dai ba dai wannan ne karo na farko da suka taba rikici har aka sasanta su ba, amma dai ba a taba batun zuwa kotu ba sai wannan karon.

Sai dai duk wannan rikici da ke faruwa tsakaninsu, a duk lokacin da aka tuntubi Ali Nuhu ba ya cewa komai.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

Ko a rigimar zuwa kotun ma, an tuntube shi kuma ya ce ba zai tofa komai ba sai dai a ji ranar zaman kotun.

Cikin wata hira da ya yi da manema labarai akan batun kai masa sammacin, Adam ya kara da cewa: “Da na yi rubutu na zagi Ali ba alfahari nake da hakan ba, na san ba daidai ba ne.

“Sai dai daga bisani na fahimci abin da na yi ban kyauta ba, da nemansa na yi gaba da gaba na gaya masa maimakon shaida wa duniya.

“Amma na yi hakan ne saboda wadanda suka zage ni a dalilinsa su ma sun yada ne duniya ta gani.”

Daga bisani dai an sasanta jaruman biyu da suka kasance na kut da kut a da.

“Amma daga baya manyanmu sun zaunar da mu sun sasanta mu, kuma na ba shi hakuri.

“Sai dai kamar yadda aka sa na ba shi hakurin nan, ai ya kamata shi ma a kalla ya sa yaransa masu zagina su ba ni hakuri ko da sau daya ne,” in ji Zango.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.