Wasanni

Ban Ji Dadin Hana Ni Zuwa Wasannin Olympics Ba, In Ji Salah

Shahararren dan wasan tawagar kasar Masar kuma kaftin din kasar, Mohammad Salah, ya bayyana rashin jin dadinsa bisa matakin da kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta dauka na hanashi halartar gasar cin kofin kwallon kafa na wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya wato Olympic.

Tun a kwanakin baya aka kawo rahoton cewa babu wani dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ko daya da zai halarci wasannin Olympic da za’a fafata a babban birnin kasar Japan watoTokyo, wasannin gasar da za su kankama a wannan watan bayan da tun farko annobar cutar Korona ta tilasta aka dage gasar daga shekarar data wuce zuwa wannan shekarar

A wani sako da kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta aikewa kasashen da ‘yan wasanta ke buga mata wasa, ta ce bata fatan bai wa kowanne dan wasa damar takawa kasarsa wasa a wasannin na Olympic ciki har da Mohammed Salah na kasar Masar wanda kasar sa ke maitar ganin ya buga mata wasannin domin lashe kofin.

Za dai a fara wasannin na Olympics da cutar Korona ta hana bara ne a ranar 22 ga wannan na watan yuli kuma karkare a ranar 7 ga watan Agusta kamar yadda kwamitin shirya gasar ya tsara tun a farkon wannan shekarar duk da cewa an tabbatar da cewa za’a budanar da gasar babu magoya baya saboda cutar Korona.

Sai dai duk da sakon na kungiyar Liberpool shugaban hukumar kwallon kafar Masar Ahmed Mujahed ya bayyana fatan dan wasan ya iya samun alfarmar takawa kasar wasa saboda a cewarsa suna bukatar kawarewar Salah a gasar.

“Naso buga wannan gasar saboda tana daya daga cikin wasannin da nake son ganin ina fafatwa amma duka matakin da kungiyar da nake bugawa yayi daidai kuma tuni na koma daukar horo’ in ji Salah

Mohammad Salah mai shekaru 29 a duniya fiye da shekara guda kenan ana dambarwa kan yiwuwar ya rasa damar takawa kasar tasa wasa a wasannin na Olympic kuma a cewar Mujahed ba ya tilastawa Salah ya bugawa Masar wasa a wasannin gasar amma abu ne mai matukar wahala ga kasar da shi kansa dan wasan, a iya zuwa gasar ba tare da shi ba.

Har ila yau, baya dan wasa Salah ‘yan wasa irinsu Minamino da sabon dan wasan kungiyar, Ibrahim Konate dukkaninsu ba zasu samu damar bugawa kasashensu wasannin ba kamar yadda kungiyar kwallon kafar ta Liberpool ta bayyana.

#hausaleadership

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: