Ban Ga Laifin Sarki Sanusi II Ba Don Yana Magana Kan Abun Ya Dace Ya Sa Baki Gane Da Jihar Kano


0 177

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Yasir Ramadan Gwale

Mafiya yawan mutanen Kano, kusan zaka iya cewa kaso 80 na al’ummar Kano, an haifesu ne zamanin Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero, mutane da dama basu san Sarauta ba sai ta Sarki Marigayi, shi yasa da yawa suke ganin duk yadda Sarki marigayi yayi haka ake Sarauta.

Shi Sarkin Kano marigayi, Allah ya yi shi mutum mai zurfin ciki, mai kau da kai, baya magana sosai, ance yana da kawaici har da barin abinda yake halalinsa. Wannan muma halinsa ne kuma dabi’arsa ce haka.

Da yake bamu riski zamanin Sarakunan baya ba, da suka yi mulki kafin marigayi Ado Bayero, amma kuma mun karanta a tarihi, cewar Sarki Kano Muhammadu Sunusi I da Sarkin Kano Muhammadu Inuwa ba mutane ba ne da suke shiru, suna da yawn zance akan batun mulki da Shugabanci.

Don haka, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, ba wani sabon abu bane dan yayi magana akan abinda yake ganin ya dace a ji bakinsa akai. Domin kowa akwai yanayin da Allah ya yishi.

Kamar yadda yake hali ne na Sarkin Kano marigayi, yin shiru da rashin son magana, shi kuma Sarki na yanzu ba dabi’arsa bane yin shiru akan abinda yake ganin ya dace yayi magana.

Kowanne dan Adam da yadda Allah ya yishi, babu kuma yadda za a ce tilas sai wani ya zama wani da ba shi ba. Akwai wanda shirunsa kuskure ne, akwai kuma, wanda yin shirunsa alheri ne.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Ba yadda za ai Mai Martaba Sarkin Kano da Allah ya huwacewa tarin ilimi dama da hauni, yasan kabli, yasan ba’adi, ya san duniya, duniya ta sanshi, kawai yaja amawali yayi dinkim, alhali maganganunsa da yawa zasu janyo alheri ga al’ummar Kano dama Najeriya.

Mai Martaba Sarki dan adam ne kamar kowa, zai iya yin daidai zai iya kuskure. Da yawan mutane sun saba ne da salon mulki irin na Sarkin Kano marigayi, shi yasa duk abinda suka gani da ya saba da nasa, suke ganin kamar ba daidai ba ne, alhali kuwa shi dabi’arsa ce haka.

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, uban kowa ne a Kano, ya dace ya sanya bakinsa akan duk abinda ya shafi jihar Kano dama Najeriya baki daya, indai batu ne na al’umma da cigabansu.

Mai girma Gwamna, wa’adin mulkinka nan gaba shekaru hudu ne idan muna raye, dukkan wadan da zasu yi amfani da damarsu ta samun kusanci da kai su zugaka kan batun masarautar Kano da Sarkin Kano kan abinda suke gani na sabani tsakaninka da shi, ba masu kaunarka bane, mai girma Gwamna ka bayar da dama wasu sun yi maka ingiza mai kantu ruwa.

Babban abinda yafi damun mutane musamman a cikin birnin Kano, bai wuce rashin samun ruwan amfanin yau da kullum ba, da yawan mutane a cikin Kano sun dogara ga ‘yan garuwa masu tura kura wajen samun ruwa, ko borehole ga mawadata, inama ace akan haka mai girma Gwamna ya maida hankali, yayi kiran majalisa tayi zaman gaggawa dan magance matsalar ruwan sha a Kano.

Mai girma Gwamna kada a zugaka kayi kunu nan gaba kazo kana shan kunu. Allah ka zaunar da Kano lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
04-09-1440AH

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.