Ra’ayin Zainab Muhammad Nura
Gaskiya ni dai Wallahi raina ya baci sosai lokacin da na ji labarin wai an bada belin mutane 20 da ake zargin sun kashe Janar Alkali, ko wata uku ba su yi ba amma gashi Malamin Shi’a Zakzaky yau shekara uku yana kulle kuma wata kotu ta bada belin shi amma an ki a sake shi.
Shi Zakzaky ya kashe wani ne? Ko saboda shi Musulmi ne kawai. Me ya sa aka hana shi beli aka ba wa masu kisa?
Dama kwanaki ana zargin Gwamnan garin ya zo yana rokon a yafe musu har wasu suna yin musu, to gashi alama ya fara tabbatuwa.
Gaskiya musalman arewa mu hada kai idan yau wani ne gobe hala kaine, shugabanni su yi wa kowa adalci sai a zauna lafiya kawai.