Babu Wani Sauran Mai Tunani a Jam’iyyar PDP – Gwamna El-rufai
Gwamnan jihar Kaduna Gwamna Nasiru El-Rufai ya mayar da martani ga jam’iyyar inda ya yi kaca-kaca da jam’iyyar da cewa babu sauran wani mai tunani da ya rage a jam’iyyar a yanzu.
Gwamnan dai ya mayar da martani ga jam’iyyar ta PDP ne wanda da a farko ta caccake shi biyo bayan kalamansa wanda ya ambaci tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da ke zaman mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019.
Gwamna El-Rufai ya yi kalamai akan Mista Peter Obi inda yace shi mai tsananin kabilanci ne, ya jawo cece-kuce da zafafan kalamai daga al’ummar Nijeriya din wanda hakan ne ma ya sa jam’iyyar ta PDP ta fitar da sanarwa dauke da martani zuwa ga gwamnan.