Labarai

Babu Wanda Zai Iya Zargi Na Da Cin Hanci Da Rashawa, Inji Shugaba Buhari

Daga Ibrahim Da’u Mutuwa Dole
Shugaba Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa halin nuna wariya da rashin adalci da ke tattare da kasar nan ba kabilanci ko addini ne ke rura wutar ba, illa su kansu ’yan Nijeriya.

Buhari ya fadi hakan ne yayin karbar mambobin kungiyar Muhammadu Buhari/Osinbajo Dynamic Support Group kwanan nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A cewarsa, babu wanda zai tuhume shi da rashawa bayan ya yi gwamna, minista, shugaban kasa kuma a halin yanzu ya zama Shugaban kasa a karo na biyu.

Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya yi cikakken jawabin da Shugaban ya yi wa baƙinsa ga manema labarai a ranar Laraba a ƙarƙashin taken ‘’ Ka manta da ƙabilanci, ka manta da addini. Mu mutane, mu ne matsalar Najeriya, in ji Shugaba Buhari ’.

Ya ce, “Matsalarmu ba ta kabilanci ko addini ba ce ta kanmu ce”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: