Babu Inda Nace Kuri`ar Yan Izala Ta Isa Buhari Yaci Zabe -Kabiru Gombe

2

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babu Inda na taba furta cewa “Iya Yawan Kuri’un ‘Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri’un ‘Yan Darika, Cewar Sheik Kabiru Gombe.

Ya kuma kalubalanci a kawo muryarsa inda ya fadi haka

Talla

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Shahararren Malamin nan Sheikh Kabiru Gombe yace bai taba furta cewa “Iya Yawan Kuri’un ‘Yan Izala Ya Ishi Buhari Ya Ci Zabe ba, Don Haka Ba Ma Bukatar Kuri’un ‘Yan Darika” Shehin Malamin yace wannan karya ce da kirkiran Labarin karya irin na ‘Yan shi’a.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 14

“Duk wa’azin da IZALA take gabatarwa akwai kaset na wa’azin, dan haka mun Kalubalanci wadanda suka kirkiri labarin dasu saka Murya ko Video na inda muka fadi haka, in kuma basu kawo ba zaku gane cewa zunzurutun makaryata ne “Inji Shi”

Kazalika ana kara Jan hankalin mutane da su kara lura tunda zabe ya kusa zuwa, makiya sun dinga kirkirar labaran karya suna yadawa akan Malaman Sunnah, saboda kiyayyar su da Sunnah, da kuma shugaba Buhari, amma ta Allah ba tasu ba.

Dan Haka shehin Malamin ya nemi jama’a da suyi watsi da wannan zancen, kuma yace IZALA tana nan akan matsayarta na zaben shugaban kasa ranar asabar a futo a zabi Muhamnadu Buhari, jihohi kuma su zabi abun da suke so a zaben gwamnoni dan maslahar jahar su.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: