Babbar Nasara: ‘Yan sanda sun ceto ɗaliban jami’a tarayya ta Gusau biyar da aka sace a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta ce ta ceto ɗalibai biyar na Jami’ar Gusau bayan sace su da masu garkuwa suka yi.
Kwamashinan ‘Yan Sanda Mohammed Bunu ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Juma’a cewa wasu mutane ne ɗauke da makamai suka afka gidan wani mai suna Isah Mai Burodi a yankin Sabon Gari na ƙauyen Damba.
Ya ce maharan sun kuma ƙwace kuɗi N200,000 daga gidan mutumin, inda suka wuce gidan ɗaliban tare da sace maza biyu da mata uku.
“Muna samun rahoton lamarin, dakarunmu suka bazama kuma suka ceto mata biyu; Blessing Matthew da Comfort Olola.” in ji shi.
Ya ƙara da cewa daga baya sun sake kai samame dajin Karazau kuma da ganinsu ‘yan fashin suka arce tare da barin sauran ɗaliban da suka yi garkuwa da su.
Add Comment