-Advertisement-


Babbar Matsalar Da Nake Fuskanta Wajan Taimakawa Marasa Karfi -Mansura Isah


0 413

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

– Shugabar gidauniyar ‘Today’s Life Foundation’, Mansurah Isah ta bayyana irin nasarorin da gidauniyar ta samu tun bayan kafa ta

– Matar Jarumi kuma mawaki Sani Danjah ta ce, kalubalen da take fuskanta a wasu lokuta kan sa ta fara tunanin rufe gidauniyar da fatan wanda tayi ya hau mizani

– Tayi kira ga masu hannu da shuni da su dinga kai ziyara asibitoci ko wuraren da mabukata suke don tallafawa jama’ar Annabi

Shugaban gidauniyar tallafawa mabukata da marasa lafiya mai suna ‘Today’s Life Foundation’, Hajiya Mansurah Isah ta bayyana irin tarin matsalolin da take fuskanta a wajen aikin tallafawa jama’a.

Ta ce hakan na sa wani lokacin ta ji kamar ta dakatar da wannan fafutukar, da fatan wanda tayi Ubangiji ya sanya a mizani.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Sananniyar tsohuwar jarumar Kannywood din, ta bayyana hakan ne a lokacin da take tattaunawa da mujallar fim kan irin nasarorin da gidauniyar ke samu tun bayan kafa ta.

Matar Jarumin mawaki Sani Danja, ta ce gaskiya an samu manyan nasarori tun bayan kafa wannan gidauniya, kuma dumbin mabukata sun amfana da hakan.

“Muna da bangaren samar da abincin da aka dafa ko kuma tsaba. Wannan kokarin mun yi shi a cikin birni da kauyuka, duk muna shiga domin kai wa mabukata talllafi. Bayan haka, mu kan ziyarce asibitoci domin kai wa marasa lafiya magani da kudin da zasu dan rike a hannunsu.

Bangaren mata masu haihuwa da kananan yara muka fi mayar da hankali,” cewar Mansurah Isah.

Da ta juya bangaren matsalolin da suke samu kuwa, sai Mansurah ta ce, “Abin tashin hankalin da muke fuskanta shine yadda zaka ga ana hada wa mara lafiya kudi, kafin mu kammala sai kaga Allah ya dauki ranshi, Wannan abun na matukar sa ni cikin tashin hali da firgici.”

#Hausalegit

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.