Labarai

BABBAR MAGANA: Barayi Sun Kai Hari Villa, Sun Yi Kokarin Fasa Gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Gambari

Daga Comr Abba Sani Pantami
Labari da duminsa na nuna cewa wasu barayi sun yi yunkurin fasawa cikin gidan shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.

Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.

“Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar da cewa an yi “wawan yunkurin” yi masa fashi a gidans misalin karfe 3 na daren nan amma basu samu nasara ba,” Garba Shehu yace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: