Gwamnatin jihar Legas ta yi odan tireloli 70 na buhuhunan shinkafa domin siyar wa mutanen jihar don bikin Sallah.
Shinkafar ‘Lake Rice’ za a fara siyar dashi daga Gobe Alhamis har sai bayan Sallah.
Kwamishinan aiyukkan noma na jihar Toyin Suarau ya ce gwamnati za ta siya da shinkafar a duk kananan hukumomin jihar.
“Za a siyar da babban buhu 50Kg akan Naira 12,000, 25Kg akan Naira 6,000, 10Kg akan Naira 2,500’’.
Toyin ya ce gwamnati tayi haka ne don ta agaza wa musulmai domin bukin sallah dake tafe.
Daga karshe Toyin Suarau ya ce gwamnati ta kara bunkasa kamfanin sarrafa shinkafa dake ‘Imota Rice Milling Plant’ da ke jihar.
Add Comment