Babban Magana: Kotu Ta Saki Wadan Da Ake Zargi Da Sanadin Kama Zainab Aliyu


0 247

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babban magana:

Kotu ta saki wadan da ake zargi da sanadin kama Zainab Aliyu, wadda kasar Saudiyya ta kama da laifin shigo da kwaya

Wata babban kotu a Kano ta bada belin mutane shida da hukumar NDLEA ta kama tare da tuhumarsu da safarar kwaya zuwa kasar Saudiyya amma suka lakaba jakar cikin tambarin jakar wata yarinya ‘yar Shekara 22, daliba a jami’ar jihar Kano, Zainab Habib Aliyu da ta je kasar aikin Umara tare da iyayenta.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Wadan da aka kaman da suka hada sa Idris Umar Shehu (alias Umar Sanda), Sani Suleiman, Nuhu Adamu, Rhoda Adetunji, Udosen Itoro Henry da kuma Sani Hamisu, dukkansu ma’aikata ne a babban tashar sauka da tashin jiragen sama ta kasa da kasa da ke Kano (MAKIA).

Mahaifin yarinyar Zainab, Alhaji Habib Aliyu, shugaban gidan Rediyon gwamnatin tarayya ne ya shigar da karan gaban kotu, inda alakalin kotun, Lewis Alagoa a ranar Litinin ya bada Belin wadan da ake tuhuma yayin da Zainab ke tsare a hanun mahukuntar kasar Saudiyya kafin sakota a jiya Talata.

Majiyarmu ta Jaridar Daily Najeriya ya ruwaito cewa, tuni har daya daga cikin wadan da aka sake din, Umar Shehu (Alias Umar Sanda) ya wuce zuwa kasa mai tsarki domin aikin Umarah.

Alhaji Habib, ya koka kan dalilin da zai gamsar da kotu har ta saki wadan da aka tabbatar da sun aikata wannan mummunan aiki. Daga karshe mahaifin Zainab ya mika godiyansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa bada umarnin daukan matakin gaggawa ga Ministan shari’a domin ceto rayuwar ‘yarsa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.