A jiya ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin a kwace wa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari miliyoyin nairori. Daga Madubi-H
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta ba da umarnin cewa kudaden dake asusun wasu kamfanoni daban-daban da ke da alaka da Yari sun kai $ 56,056.75 a Bankin Polaris; N12.9m, N11.2m, $ 301,319.99; N217,388.04 da kuma $ 311,872.15 a banki daban-daban na Zenith za a mallakawa gwamnatin tarayya su, kamar yadda shafin Twitter na jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Idan bamu manta ba, tun bayan direwar sa daga karagar mulki a shekarar 2019, tsohon gwamnan na zamfara Abdul’aziz Yari, yake fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
#Kanomedia