Ga yadda jadawalin zai kasance👇👇👇
1. Motoci za su rage tsada, an dawo da harajin shigo da motoci 5% daga 35%.
2. Babu haraji kan duk ma’aikatan da albashinsu bai wuce N30, 000 ba.
3. An daina cire wani kaso da sunan kudin hatimi idan aka aika kudi a banki, Wanda aka aika wa kudin da suka haura N10,000 ne zai biya Naira 50.
4. An rage kudin harajin da ake karba a kan kananan kamfanonin da jarinsu bai kai Naira miliyan 25 ba.
5. Gwamnati za ta kar6i aron kudin da aka manta da su a cikin banki kafin wanda ya mallake su ya dawo kansu.
6. Babu VAT a kan abincin dabbobi, kayan aikin gona jiragen sama na kasuwanci da sauran kayan jirgi.
Haka zalika babu VAT a kan kudin tafiya a jirgi. Gwamnati ta cire VAT a kan filaye da gidajen da aka saida.
7. Za a dunga kar6ar haraji a ribar da aka samu daga gudummuwa ko kyauta da gwamnati ta bada.
8. An rage mafi karancin harajin da ake kar6a a hannun kamfanoni daga 0.5% zuwa 0.25%.
9. Kamfanonin ketare za su bukaci lambar TIN, kuma za su dunga biyan haraji.
10. Za a dauke biyan haraji daga kamfanonin da ke aikin gona da noman dabbobi da kifi.
Mu na fatan Allah ya sa hakan ya zama alkairi ga al’umma da ma kasarmu Najeriya.