Babban Darakta, Falalu A. Dorayi, Ya yi Wa Ali Nuhu da Adam A. Zango Nasiha kamar haka


1 974

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babban darakta, Falalu A. Dorayi, ya yi wa Ali Nuhu da Adam A. Zango (kai, da ma mu duka) nasiha kamar haka:

H A K U R I DA A M F A N I N S A

Ubangiji (SWA) Ya halicci Yan adam masu halayya iri-iri, wasu masu saukin Mu’amala wasu masu zafi.

Lallai mu sani dukkan sha’anin rayuwa tsakanin mu, yana iya zuwa da dai dai ko akasin haka.

RASULULLAH (SAW) Ya umarce mu da mu nemi tsarin ALLAH daga sharrin kawunan mu,
da miyagun aiyukan mu.

A takaice babu wanda ya isa ya kaucewa kaddarar alkairi ko ta sharri da Allah ya rubutu masa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

- Advertisement -

Dan haka duk wata damuwa kunci/masifa da rashin kwanciyar hankali, idan bawa yai hakuri ya mika lamarin sa ga Allah, da sannu farin ciki zai maye gurbinsu.
Mu sani bin umarni Allah da Annabinsa da yiwa iyaye biyayya, kyautatawa iyalinka da Yan uwanka, yin ibada da barin aikin sabo dukka wajibine, amma sai an daure kuma anyi hakuri.

Dan uwa in ka zamo mai hkuri lada kake samu mai tarin yawa. Sannan ka sami daukaka da daraja ka zamo abin alfari abin koyi, saboda kyawun dabi’ar da hakuri ya baka.

Hakuri dashi ake zumunci.
Hakuri dashi ake kore masifa.
Hakuri dashi ake sulhu.
Hakuri dashi ake samin nagarta.

Mai neman alkairin duniya da lahira yayi hakuri domin Allah, ko da an zalinceshi yana da ikon ramawa.

Hakika Ubangiji yana tare da masu hakuri, kuma an yi tanadi na lada mai tsoka da ALJANNAH a garesu.

Allah ka bamu hakuri da Juriya akan dukkan Al’amuranmu. Amin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.