Babban Bankin Nijeriya ya bayyana cewa zai kaddamar da wasu shirye-shirye har guda biyu da nufin tallafawa tsarin Bankin Musulunci wanda zai hada da samar masu tsarin inshora na Musulunci wato, ‘Takafut’. kamar dai yadda shirin ya samu nasara a kasar Malesiya.
Wannan mataki na Babban Bankin zai samar da shinfida kan yadda Nijeriya za ta zama kan gaba wajen rungumar wannan tsarin Banki na Musulunci a Afrika wanda tsari ne da ya haramta bashi da ruwa da kuma caca.
A halin yanzu dai Bankunan ‘Sterling Bank’ , ‘ Stanbic IBTC’, da Jaiz Bank ne suka kaddamar da tsarin Bankin Musulunci inda Bankin ‘ Jaiz Bank’ ne ke tafiyar da tsarinsa gaba daya irin na Musulunci tun shekarar 2012.
Add Comment