Labarai

Babban Albishir Ga Ma’aikatan NPOWER Batch A da Kuma B

Kamar yadda sanarwa ya gabata kwanaki kadan da suka gabata cewa; Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kammala shirin sake daukan matasan da sukaci moriyar N-POWER rukunin batch A da batch B za’a shigar da su cikin wani sabon tsari da aka masa suna da NEXIT PORTAL ta hannun Babban bankin Nigeria (CBN).

Gwamnatin shugaba Buhari tayi la’akari da cewa da akwai tausayawa idan aka kori matasan da sukaci moriyar shirin N-POWER batch A da B za’a iya samun matsala, kasancewa wasu da kudin N-POWER din suke biyan kudin makaranta, wasu kuma da shi sukayi aure suke ciyar da iyalansu, wanda har zanga-zanga sukayi da suka samu labarin za’a dakatar da su.

Shirin yana gudana ne karkashin Ma’aikatar jin-kai da kula da ibtila’i da walwalar al’ummah karkashin jagorancin Minista Hajiya Sadiya Umar Faruq, ma’aikatar ta fitar da sabon link ga wadanda suke cikin tsarin N-POWER batch A da batch B kadai, domin su cika a shigar da su cikin sabon tsarin NEXIT PORTAL wanda za’a fara biyansu da shi, ga link din kamar haka https://nexit-fmhds.cbn.gov.ng/auth/signup

Don Allah duk wanda aka san yaci moriyar N-POWER batch A da batch B a sanar dashi ya cika wannan sabon tsarin na NEXIT PORTAL da za’a shigar da su, wanda bai cika ba shikenan yayi asara.

Bayan haka, nan da kwanaki kadan masu zuwa za’a fitar da sunayen wadanda suka cika N-POWER batch C sukayi nasara.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: