Wasanni

Ba Zan Yi Ritaya A Yanzu Ba – Messi

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da tawagar kasar Argentina, Leonel Messi, ya bayyana cewa zai ci gaba da buga wasan kwallon kafa nan da shekaru masu yawa duk da rade radin da ake yi na cewa zai iya ajiye takalmansa nan gaba kadan.

Dan wasan ya sanar da haka ne a wata hira da yayi da manema labarai a kasar Brazil a ya yinda ake ci gaba da buga wasannin cin kofin Coppa America da kasar ta Brazil take daukar nauyi.

A kwanakin baya shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Joan Laporta ya tabbatar da cewa shahararren dan wasan zai ci gaba da buga wasa a Barcelona, sai dai har yanzu ba su cimma matsaya ba akan sabon kwantiragin dan wasan sai dai laporta yana fatan Messi zai saka hannu kan kwantiragin da suka gabatar masa.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa akwai tayin kwantiragi mai tsoka da manyan kungiyoyi ke son yi wa dan wasa Messi ciki har da kungiyar Paris Saint-Germain sai dai ana cewar Messi zai ci gaba da zama a Sifaniya ne saboda irin alaka mai kyau dake tsakaninsa da shugaban na Barcelona na yanzu.

Tun lokacin da yafara buga kwallo a duniya, Messi kungiya daya ya buga wa wasa wato Barcelona tun yana matashi, yanzu yana yi wa tawagar Argentina gasar Copa America da Brazil ke karbar bakunci sannan shi ne kan gaba a ci wa Barcelona kwallaye a tarihi, kuma na daya a yawan buga wasanni fiye da kowanne dan kwallo da aka yi a kungiyar.

Messi ya lashe kyaututtuka da yawa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ciki har da lashe Ballon d’Or guda shida sannan ya taimakawa kungiyar ta lashe kofunan zakarun turai da kofunan La liga.

Messi dai ya so barin Barcelona a shekarar data gabata, daga baya ya yanke shawarar ci gaba da zama zuwa karshen kakar da aka kare kuma a kakar da aka kammala Messi ya fuskanci kalubale musamman a farkon kakar wasa, amma hakan bai hana shi cin kwallo 30 ba, shi ne kan gaba a La Liga da tazarar bakwai a raga.

Barcelona ta yi nasarar lashe gasar cin kofin Copa del Rey a kakar da ta kare karkashin jagorancin sabon kocin da ta dauka a bara daga tawagar kasar Holland, Ronald Koeman wanda kuma shi ne zai ci gaba da koyar da kungiyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: