Labarai

“Ba Zan Taba Talauci A Rayuwata Ba”: Inji Wani Mutumin Da Ya Kawata Dakinsa Tamkar 5 Star Hotel

“Ba Zan Taba Talauci A Rayuwata Ba”: Inji Wani Mutumin Da Ya Kawata Dakinsa Tamkar 5 Star Hotel

 

Wani mutum ya ƙawata gidansa mai ɗaki ɗaya da fasaha ta hanyar da ta sa ya yi kyau sosai.

 

A cikin wani faifan bidiyo da @investorjoe nya wallafa, mutumin da kansa ya yi kawata gidan da kayan ado kuma ya canza kamannin dakin da yake da datti.

 

Ingatattun kayan ado na ciki da mutumin ya nuna a cikin bidiyon ya haifar da martani tsakanin masu amfani da TikTok waɗanda suka nuna sha’awar ɗakin.

 

Mutumin ya canza kamannin dakin inda ya mayar da shi tamkar 5 Star Hotel.

 

Wani ɗan gajeren bidiyon TikTok wanda @investorjoe ya wallafa ya ɗauki yadda mutumin ya yi aikin adon cikin dakin inda Mutane da dama suka yaba masa bisa wannna adon da yayi wa daki.

 

Daga Baba Waziri Net