Kannywood

Ba Zamu Yiwa Dokar Hana Mu Yawo Da Dabbobi Biyayya Ba, Inji Fulani Makiyaya

Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta bayyana cewa, ba zata yiwa dokar hanasu kiwon yawo da dabbobi ta gwamnonin Kudu biyayya ba.

Ƙungiyar tace wannan doka sheɗaniyar doka ce kuma bata da muhalli a kundin tsarin mulkin Najeriya.

A ranar 1 ga watan Satumba ne dai dokar ta hana kiwo ta jihohin Kudancin Najeriya zata fara aiki.

Miyetti Allah ta bayyana cewa idan gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sauka daga muƙaminsa, sai sun kama shi.

Sakataren ƙungiyar, Saleh Alhassan ne ya bayyana haka ga manema labarai na Leadership.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: