Get New DJ Mixes
Labarai

Ba Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa Ba 2019 A PDP – Jonathan

-‘Yan Jam’iyyar PDP masu mata zagon kasa ne suke yada jita-jitar cewa Jonathan zai tsaya takara

PDP zata fitar da dan takaran shugaban kasa ne daga Arewa

Zagi da kushe da hassada ba zai dusashe tauraron Goodluck Jonathan ba

Shiyyar kudu maso kudu ta jam’iyyar PDP ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai fito takaran shugabancin kasa ba a 2019.

Kungiyar ta fadi hakan ne a yayin karyata cewan Jonathan zai mamaye jam’iyyar ta bangaren jihar Bayelsa don manufar sa ta fitowa takaran shugabancin kasa.

 

Jagoran wannan kungiya Ariolu Tebidafa (dan jihar Delta) da sakataren ta Akpan Ibibio (dan jihar Akwa Ibom) sun ce ‘yan kungiyar masu mata zagon kasa ne suka yada wannan jita-jita.

Sun ce PDP zata fitar da dan takaran ta ne daga Arewa.

Sun kuma yi kashedi akan neman batawa tsohon shugaban kasan suna.

Sun kara da cewan ”Idan tsohon shugaban kasa yana da wani ra’ayi to bai wuce akan wanda zai Jagoranci jam’iyyar a matakin koli ba don ciyar da kasan gaba”.

”Wannan ba komai bane illa kawar da hankalin tsohon shugaban kasa a yayin da yake tarayya da shuwagabannin kungiya da mayar da hankalin sa wurin kimtsa jam’iyyar mu don fuskantar zabe mai zuwa”.

‘Kudu maso kudu suna alfahari da tsohon shugaban kasa bisa ga ayyukan da yayi wa kasa lokacin shugabancin sa da kuma yadda ya hakura da mulki don zaman lafiyar kasan.

A tunanin mu yabo da girmamawa ya cancance shi”.

”Zagi da kushe da hassadan mahassada ba zai taba dusashe tauraron tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba”.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.