Ba Za Mu Zuba Ido Mu Ga Ana Cin Zarafin Yara Da Sunan Bara Ba, Cewar Gwamnatin Kaduna

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A kokarin gwamnatin jihar na ci gaba da yakar cutar corona da yawon, hukumar yaki da cutar ta corona ta yi nasarar ceto yara kimanin 160 daga wuraren da suka saba doka. Yara ‘yan asalin jihohin 13 ne da suka fito daga kudu da Arewacin Nijeriya. Wasun su ma bakin haure ne daga kasashen Benin, Burkina Faso da Nijar.

Wurare da aka bankado yaran an gano sun saba dokar rufe makarantu don gudun yaduwar cutar corona da aka kafa tun a watan Dimsaba, 2020. Haka kuma dokar ta shafi yunkurin gwamnatin Kaduna na mayar da almajirai jihohin su na asali domin ci gaba da neman ilmi a gaban iyayensu.

Gwamnatin Kaduna tana mai tunatar da kungiyon masu zaman kan su, shugabannin addinai, cewa tana da dokoki da sharruda na bada damar gudanar da neman ilmin yara ga makarantun da suka yi rijista. Domin ganin su ma almjirai an kawata sha’anin karatun su kamar sauran yara masu gata.

Rahotanni sun nuna cewa tun daga watan Maris, 2020 zuwa yanzu, gwamnatin Kaduna ta kama yara almajirai kimanin dubu 31,092, inda ta mayar da su zuwa jihohin su, tun bayan da gwamnonin Arewa suka kudiri aniyar dakile cin zarafin da ake yi wa yara da sunan almajiranci. Wanda kuma tun daga wannan lokacin ne gwamnatin ta dukufa wajen zakulo irin wuraren da ake kange yara tana ceto su tana mayar da su wurin iyayensu domin ci gaba da neman ilmi a gabansu.

Biyo bayan wannan tsari, gwamnatin Kaduna ta ceto yara 1,118 daga jihar ta mayar da su jihohinsu na asali.

Haka kuma a yayin sintiri makamancin haka da hukumar da ke da alhakin ceto yaran suka fita a makon da ya gabata, sun ceto yara 160 wadanda kuma tuni aka gano jihohinsu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 747

Daga cikin su akwai ‘yan jihar Kebbi guda 16, Abuja 2, Kano 15, Katsina 15, Zamfara 8, Sokoto 1, Nasarawa 12, Neja 5, Kwara 4, Kogi 2, Oyo 2, Kaduna 68.

Sai kuma yara bakin haure daga kasashen Nijar (5), Burkina Faso (3) da Benin (1).

Yanzu haka an killace yaran domin duba lafiyar su game da cutar corona daga bisani kuma a mayar da su jihohin su na asali.

Gwamnatin Kaduna ta kuma yi kira ga iyayen yara da su kasance masu baiwa ‘ya’yan su duk wani hakki na tarbiyyantarwa kamar ba su ingantaccen ilmi, ciyarwa, tufatarwa, domin yin watsi da yaran ya sabawa addini da al’adunmu. Sannan kuma ya sabawa dokar kasa ta baiwa yara ilmi, dokar walwalar yara da kuma dokar tallace-tallace. Don haka dole ne hukumomin da suke da alhakin dakile matsalolin su ci gaba da aiki tukuru domin kawo karshen matsalar.

Sanarwar hakan ta fito ne daga mai taimakawa Gwamnan Kaduna kan harkokin yada labara,
Mista Muyiwa Adekeye

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: