Labarai

Ba za mu yi Hawan Sallah ba saboda rashin tsaro – Msarautar Daura

Masarautar Daura ta dakatar da Hawan Sallah a bikin Babbar Sallah da za a yi a mako Mai zuwa

Wata sanarwa da “Jihar Katsina a Yau” ta samu wacce Danejin Daura Abdulmumini Salihu ya fitar a Yau Talata ta ce Sarki Umar Faruq Umar ya ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin masarautar.

“A maimakon haka, za a gudanar da Sallar Idi kamar yadda aka saba, bayan an kammala za a gudanar da addu’o’i na musamman a fadar mai martaba sarki don neman dawwamammen zaman lafiya,” in ji sanarwar.

Al’ummar Musulmi a Najeriya za su gudanar da bikin Babbar Sallah ranar 10 ga watan Zul Hijja na shekarar Hijira ta 1442, wanda ya yi daidai da 20 ga watan Yuli.

© BBCHAUSA/

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: