Labarai

Ba Za Mu Yarda A Mayar Da Kano Cibiyar Zagin Sahabban Annabi S.A.W ba

Sakon Khalifan Qadiriya, Sheik Qaribullah Kabara Ga Gwamnatin Kano

Daga Indabawa Aliyu Imam

Khalifan Qadiriyya na Afrika kuma fitaccen malamin addinin musulunci Dakta Qaribullahi Nasiru Kabara Amirul Ansar yayi Allah wadai da shaidanun da ke aibata sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi wa sallam a cikin garin Kano.

A yayin karatun Darulhadith na mako-mako da ake yi, Khalifan ya bayyana cewa kwadayi ne ya haifar da abin da a ke yi a Kano na zagin sahabban Annabi S.A.W da magabata na kwarai.

“Sahabban Annabi sune sarakunan Muminai, yau a Kano sai a kama sunan guda daga cikinsu a zaga, gobe ma a sake yi tun daga kan sayyadina Abubakar Allah ya kara masa yarda balle kuma su sayyadina Mu’awiyya. Mahaifinmu Maulana Amirul jaishi yayi qasida baiti tamanin da uku, baki dayan qasidar tawassuli yake da sahabban manzon Allah tare da neman haduwa da su a kan manufarsu. Abin da ke ba ni mamaki da tsoro, ya yi wannan qasida ne a farkon rayuwarsa, amma bai dakko ta ya gargadi mutane ba sai a karshen rayuwarsa wanda ya yi wasiccin cewa a kula da ita.

Abin da mahaifinmu ya kare rayuwarsa yana karantarwa tare da dora mutane a kai yau a wayi gari wani shaidani ya zaburo don ya rushe wannan abu, a dinga tara ‘ya’yan mutane ana koya musu zagin sahabban Annabi S.A.W da wadanda suka yi wa sunnar Annabi aiki musamman irinsu Imamuna Bukhari wadanda a kan abin da suka yi aka gina musuluncin, yau shi ake so a ruguza, kuma ana share su Bukhari to an share musulunci baki daya.”
Cewar Khalifa Qaribullah

Khalifan ya jaddada cewa” Abu biyu ne suka haifar wa shaidanin nan abin da yake yi, na farko kwadayi wato neman abun duniya, in dai duniyar za ta samu komai zai faru ya faru, abu na biyu kuma toshewar basira, saboda duk wadannan hadisan da ake juya ma’anarsu a birkita su don a ci mutuncin sahabbai duk mun karanta su a nan, don Allah akwai wanda ya taba fahimtar irin abin da suke fada? Akwai musulmin da abin da suke fada yake zuwa tunaninsa? Saboda toshewar basira sai a juya ma’anar hadisai da ganganci abin da kowa ke ganinsa a fili sai a juya shi a mayar da shi wani abu daban kuma saboda an mayar da ku mahaukata ku hau ku zauna a kan abin da aka fada muku.

Shi Jemage ba ya gani a cikin hasken rana sai duhu ya shigo. Kenan sai Jemage ya ce babu hasken rana saboda shi ba ya ganinsa bayan matsalarsa ce ta haifar masa da hakan. Don kai ba ka fahimta ba masu hankali sun fahimta.”

Haka nan ya kara da cewa” Wannan bayani amana ce a kan kowanne musulmi, idan za ka shekara miliyan kana zagina ba ka isa na kalle ka ba balle na maka martani. Amma muddin za ka taba Allah ko Manzon Allah ko salihan bayin Allah dole na yi magana na fito da gaskiya, kuma wannan amana na kan limamai da sauran malamai su yi ta kokarin nusar da iyaye hadarin da ke cikin zagin sahabbai su hana ‘ya’yansu shiga wannan musiba.

Su masu mulkin da suka zira Ido suka bari ake irin wannan abu saboda bai shafe su ba, su sani bala’in da ke cikin abun wallahi ya fi karfin Kano, kasar ce ma za ta iya wargajewa baki daya, don ba a rushe daki ragaya ta zauna. Wadannan mutanen da ake ci wa mutunci Allah ba shi da kamar su Allah ya yi alkawarin zai zama ma’ishi ga Annabi da sahabbansa a Alqur’ani.

Abin bakin ciki ne a hedikwatar musulunci kamar Kano a dinga zagin sahabbai da magabata na kwarai amma shugabanni su kawar da kai don kawai ba su ake tabawa ba.

Ku yi addu’a duk wanda ke taimakon wannan lamari ko wanda yake da hannu a cikinsa ku yi masa addu’a Allah ya zare albarka cikin lamarinsa, ya sa masa bakin jini a cikin al’umma, kuma Allah ya hana shi abin da yake nema.

Muna da bambancin fahimta, amma munyi ittafaki a Kano ba zamu yarda a mayar da ita cibiyar zagin sahabban Annabi S.A.W ba.” Inji Khalifan Qadiriya Malam Kabara.

Tun da jimawa ne dai al’ummar musulmi a kasar nan musamman Kano ke kiraye-kiraye ga gwamnatin ta Kano da ta dauki mataki a kan Abduljabbar Kabara bisa zarginsa da suke yi yana cin mutuncin Annabi S.A.W sahabbansa, matansa da magabata na kwarai, kamar yadda suka zarge shi da karyata Alqur’ani da karbo kwangilar rushe addinin musulunci sai dai Abduljabbar Kabara ya yi martani ga zarge-zaren.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: