Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yi tir da Allah wadai da yin garkuwa da fasinjojin 20 a kauyen Kundu dake kan hanyar Zungeru a jiharsa.
A wata takardar manema labarai da jami’ar yada labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta sanya wa hannu jiya, ta ce, Gwamna Bello ya bayyana wannan harin ’yan bindigar a matsayin rashin hankali da gwamnatinsa ba za ta lamunce shi ba, tana mai karawa da cewa, gwamnatin sa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Gwamnan ya ce, gwamnatinsa ba za ta mika wuya ga ‘yan ta’adda ba, musamman masu garkuwa da jama’a.
“Za mu cigaba da amfani da dan abinda mu ke da shi wajen karya lagonsu,” inji shi.
Awani Sabon rahotan da mukasamu na Cewa Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello nacewa Garkuwa Da Daliban Kagara: Ba Zai Bada Fansar Ko Sisi Ba
Kwana daya bayan rahoton garkuwa da dalibai, da malamai na makarantar sakandire ta gwamnati a Kagara dake karamar hukumar Rafi jihar Neja; Gwamna Abubakar Sani-Bello na ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta biya fansa ga masu Garkuwa Da Mutane ba.
Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba, bayan sace wasu dalibai da ma’aikatan Kwalejin a daren jiya Talata.
Ya kuma nuna rashin jin dadinsa akan matsalar tsaro dake addabar jiharsa, amma ya bada tabbaci ga jama’ar jihar za su cigaba da hada hannu da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an tsaro akan yaki da ‘yan ta’addar wajen kawo zaman lafiya ga jama’a. inda Yake Cewa gwamnati ta shirya jami’an tsaron da za su fuskanci maharan cikin Gaggawa.
Ya ce, “Ina jin zafin matsalar tsaron da ke damun jihar nan. Burina shi ne tsare rayuka da dukiyoyin jama’a, ba abinda ba za mu dawo da shi kan turba ba.
Ina goyawa ayyukan jami’an tsaron baya, don ganin mun kare hanyoyin da yankunan karkara daga harin maharan.”
Ya jawo hankalin ‘yan uwa da masoyan wadanda harin ya rutsa da su da kada su karaya akan lamarin, kuma su cigaba da addu’ar Allah ya dawo da su gidajensu lafiya.
Gwamnan ya nemi jama’a da su cigaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai wajen bada bayanan da za su taimaka wajen ceto wadanda aka yi garkuwan da su.
Muna Rokon Ubangiji Allah ya rusa gungun yan Ta,addan Najeriya Da masu Daukar Nauyin ta,addancin su.