Wasanni

Ba Za Mu Jefa Barcelona Cikin Bala’i Ba Saboda Messi, Inji Laporta

Daga Sulaiman Ibrahim,
Shugaban Kungiyar Barcelona ta Sifaniya, Joan Laporta ya ce, kungiyar ba za ta iya ci gaba da rike Lionel Messi ba ganin cewa kungiyar tana fama da barazanar koma-bayan tattalin arziki.

“Ba zan jefa kungiyar cikin bala’i ba ta hanyar sabunta kwantiragin dan wasan a Nou Camp.” Laporta Ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai a ranar Jumu’a.

Laporta ya kara da cewa, yunkurin ci gaba da rike Messi zai iya jefa kungiyar ta Sifaniya cikin wata kasada ta tsawon shekaru 50.

Kungiyar Kwallon kafa ta PSG ta Faransa da Manchester City ta Ingila sune gaba wajen dauko gwarzon Dan kwallon Wanda ya lashe Ballon d’Or har sau shida.

Messi ya jefa kwallaye har guda 672 a raga a wasannin da ya buga wa Barcelona, sannan ya lashe mata kofunan La Liga guda 10, kofunan zakarun Turai guda hudu da kuma Copa del Rey guda bakwai.

Babu wani dan wasa da ya taba kafa tarihin da Messi ya kafa a kungiyar ta Barcelona, inji Laporta

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.